Jagoran hakarmuslunci a Nigeria shaikh Yaaqub Ibrahim El’zakzaki ya bayyana cewa lokacin kadaici ga Imam Ridha (As) ya zo karshe
Jagoran ya fadi haka ne a wajen taron kasa da kasa na Imam Ridha karo na 13 da ake gudanarwa a birnin Mashahad na kasar Iran , haka zalika ya nuna cewa kamar yadda yazo a cikin tarihi Imam ridha yana cikin kadaici kuma yayi shahada a kadaici amma yanzu yanayi ya canza domin shi yanzu baya cikin kadaici don zamanin kadaicinsa ya zo karshe domin za mu iya bugan kirji muce yanzu kurar kadaici ta kau don da yawa daga cikin musulmi a Nigeria sun sanshi,
Daga karshe jagoran ya nuna cewa tutar dake kan kubbar haramin Imam ridha (As) da aka kai Nigeria a shekarar da ta gabata da yanzu haka aka sanya ta a samar hasumiyar Hussainiyar baqiyyatullah dake birnin zaria da dubban mutane suka taru wajen bukin sanya tutar da aka kwashe kwanaki 3 ana yi ya kara wayar da kan alumma game da matsayin Imam Ridha (As).288